Wednesday

Home Daga karshe : An Yanke shawarar korar Abdul-aziz Yari daga Jam'iyyar APC
Kwamitin da Jam’iyyar APC ta nada domin bin diddigin matsalolin da jam’iyyar ta fada da kuma mummunar kayin da ta sha a zaben 2019 ta mika rahoton ta.

Kwamitin ta ce irin yadda tsohon gwamnan jihar AbdulAziz Yari ya ja ragamar jam’iyyar na daga cikin babban dalilin da ya sa aka yi ta samun matsaloli a jam’iyyar da ya kai ga har ta sha kasa a zabukkan a aka yi a baya.

KU KARANTA WANNAN :- Kwana Casa'in - Kashi Na Sha daya 11 - AREWA24  

Baya ga shi, kwamitin ta ce ta samu rahotannin yankan baya da mataimakin jam’iyyar APC na kasa reshen Arewa, Sanata Lawal Shuaibu ya rika yi wa jam’iyyar.

sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, Mohammed Bakyasuwa ne yayi wannnan bayani da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

” Ina so kowa ya sani cewa tsakanin mu da ‘yan bangaren tsohon gwamna Yari ba’a ga maciji yanzu domin kuwa anja layi. Yari ne shafaffen da ya jefa jam’iyyar mu cikin matsalolin da muka fada a yanzu.

” Yanzu dai mun dauki matsaya daya dukkan mu cewa daga yau, mun kori AbdulAziz Yari a APC, da Sanata Lawali shu’aibu. Kowa ya sani kuma wannan shine matsayar mu ‘yan jam’iyyar APC na Zamfara.

Idan ba a manta ba an yi ta kai ruwa rana tsakanin mambobin jam’iyyar APC a jihar Zamfara a lokacin zaben fidda gwani na ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2019 da a karshe wannan matsala da suka rika samu ya kai su ga fadawa a zabukan da aka yi.

Kotun koli ta kori dukkan wani dan takara na APC daga jihar Zamfara bayan kara da sanata Kabiru Marafa ya shigar .

A karshe dai APC ta tashi a tutan babu wadda ko dan majalisar jiha daya bata iya samu ba saboda sakaci da handamar tsohon gwamna Yari.

SOURCE PREMIUMTIMES-HAUSA

No comments:
Write Comments