Friday

Home › › Duk tsuntsun da ya ja ruwa: Kasar Iran ta gargadi Trump a kan maganar yaqi
Ministan harkokin wajen kasar Iran a ranar Alhamis ya gargadi Shugaban Amurka Donald Trump, kan cewa ya tafka kuskure bisa furucin da ya yin a cewa yaqi tsakanin kasarsa da Iran ba zai jima ana yinsa ba ko da anfara.

Labarin kwanan nan kan abinda ke faruwa tsakanin Iran da Amurka shi ne, wata majiyar diflomasiyya daga birnin Vienna ta ce, Iran ta aminta da cewa ba zata ta kara yawan makamanta na uranium ba a yanzu, labarin da ya sha bambam da aniyarta ta da.

KU KARANTA:Bidiyo : Wata mata ta kashe mijinta ta yi yunkurin kone gawarsa. 

Bugu da kari kasar Iran na da kudurin kara nauyin makamashin uranium na nukilya daga kilo 300 zuwa sama kadan. Amma sai dai wannan kuduri bai cikin yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a shekarar 2015, wanda Amurka ta zare jikinta daga ciki a watan Mayun 2018.

“ Ba yanzu za su kara nauyin ba" , inji majiyar diflomasiyyar, kamar yadda ta shaidawa AFP a Vienna a lokacin da ake shirin gudanar da wata ganawa ta musamman kan shirin sarrafa nukiliya.
Majiyar ta bayyana cewa: “ Dalilin yin hakan kan iya kasancewa a bisa dalilin siyasa”, wannan kuma bai rasa nasaba da sanya hannun gwamnatin Nahiyar Turai wurin kwantar da tarzomar yankin Gulf.

Muhammad Javad Zarif, ministan harkokin wajen Iran ya ce: “ Gajeren yaqi da Iran abu ne wanda ba zai yiwu ba.” Zarif ya fadi wannan maganar ne a shafinsa na twitter, bayan Trump ya yi furucin cewa ba ya sha’awar yakar Iran, amma idan har ta kama sai an gwabza yaqin, “ to ko ba zai dauki tsohon lokaci ba”.

Ministan harkokin wajen Iran ya kara cewa: “ Duk tsuntsu da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka, so tari kana iya fara yaqi amma ba za kaga karshensa ba.”

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments