Thursday

Home Nadin mukamai: Aisha ta kara kwaba wa Buhari magana a fakaice
Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kara caccakar gwamnatin mijinta, wannan karon a kan nadin mukamai a gwamnatinsa.


Ta saka wani faifan bidiyo a shafinta na Tuwita inda wani dan gani kashenin Buhari a Tuwita (@ayourb) ya koka a kan yadda shugaban kasar ke bawa mutanen da basu yarda da akidansu ba mukami.

A cewar sa, " idan shugaba zai bayar da mukamai a gwamnati, yana bawa mutanen da suka yarda da akidansu ne, mutanen da zasu taimaka masa wajen kawo canjin da gwamnatinsa ke burin gani, ba haka kawai yake bayar da mukamai ga kowa ba. 

Ta yaya zaka bawa masu yakar akidar ka mukami kuma ka yi tunann zasu taimaki gwamnatin ka ta cimma burin ta ?

DUBA WANNAN: Rikici : Iran ta tarwatsa Jirgin leƙen Asiri na Amurka. 

" Ko da mutane basu ji haushin ka a kan bawa masu sukar ka mukami ba, ya kamata mu fada maka cewa mutanen da ka ke dauka domin su taya ka aiki basu yarda da akidun ka ba balle manufofin gwamnatin ka ."

Da take kara yada wannan sakon faifan bidiyo na @ayourb, matar shugaban kasar ta ce, " ba zaka iya kawo canji da mutanen da basu yarda da ajendar ka ba...ta ya ya zaka samu damar cimma manufar ka idan ka nada mutanen dake yakar manufofin ka ."
No comments:
Write Comments