Tuesday

Home Nazari Tare Da Sharhin Film Din Apocalypto

Apocalypto movie hausa review.


Rudy youngblood

JARUMAI:-
Rudy youngblood (a matsayin babban jarumi) itandehui Gutirrez (matar jarumi) Jonathan brewer (amatsayin namiji mara gamsar da iyali) morris birdyellohead (amatsayin mataimakin boss) carlos emilio baez (dan karamin yaron nan wanda suka shiga rijiya shi mahaifiyarsa) mel gibson a matsayin boss rafael velez a matsayin sarki da sauransu..

BADA UMARNI:- Mel gibson

MATAIMAKIN MAI BADA UMARNI:- adrian grunberg

RUBUTA LABARI:- Mel gibson da taimakawar farhada safinia

FURODUSA:- ned dowd

KAMFANI:- touchstone pictures tareda kamfanin Icon production

MANAZARCHI:- Shaikh Farouq Abdullahi Tukuntawa

GUNDARIN LABARI... Fim din apocalypto fim ne da yake bayani akan wasu mutane da suke gudanar da rayuwarsu cikin farin ciki da kwanciyar hankali a wani qungurmin daji mai yalwar ni'ima da manyan bishiyu tareda ruwa mai gudana da dabbobin farauta

Suna cikin wannan rayuwa ne sai Allah ya aiko musu da ibtila'i na shigowar wasu mutane marasa imani masu shiga kauyuka suna kama mutane tareda kaisu chan chikin garin su ana yanka su domin mika jininsu ga abun bautarsu

Mutanen sun kutso har wannan kauyen tareda yi musu gagarumar barna da nuna musu zallar rashin imani wajen karkashe musu mutane tareda kama sauran wanda suke raye sannan suka daura musu igiya suka tafi dasu cikin tsananin uquba izuwa inda za'a yankasu ga abin bauta

Bayan an kaisu ne har an samu damar yanka wasu daga cikin su a lokachin da ka kwantar da jarumin za'a yanka da yake Allah yasa yana da rabon sake shan ruwa a duniya sai a lokachin hasken rana ya dusashe wanda hakan yana nuna kenan abun bauta ya koshi da jini kamar yadda su wadannan miyagun mutane suka chamfa.

Duk da haka zamu iya cewa tsugune bata kare ba a wajen jarumi rudy youngblood wato jaguar paw domin kuwa wadannan mutane basu shirya qyale su ba hasali ma sai suka shirya musu wata gadar zare ta hanyar yi musu sakin talala da basu damar guduwa amma a nufin shine idan sun fara gudu susa mashi su soke su har lahira

Duk da haka Allah ya bawa jarumin nasarar tserewa tareda hallaka ƙanin boss wanda yake matukar kauna

Hakan ne ya kara batawa boss rai nan take ya bada umarnin a bishi duk inda ya shiga a kamo shi domin ya dauki fansar kashe masa qaninsa, anyi gumurzu iya gumurzu jarumi yasha bakar wahala daga karshe ya kubuta har ya isa izuwa ga wata rijiya wacce ya boye matarsa mai tsohon ciki tareda karamin dansa aciki duk da wannan tsananin wahalar matarsa ta haifa masa kyakkyawan jariri a cikin rijiya a yayin da ake tsaka da kwarara ruwan sama.

SCREENSHOTS :-

morris birdyellohead , mel gibson

itandehui Gutirrez

Jonathan brewer

carlos emilio baez


ABUBUWAN BURGEWA

Anyi amfani da zunzurutun qwarewa wajen shirya wannan fim sannan jaruman fim din sunyi kokari wajen taka rawar da ake bukata afilm din

Anyi amfani da na'urorin zamani masu kyau wajen daukar wannan fim

Yanayin shigar mutanen chiki (tufafin su) da kuma yanayin dazuzzukan ya dace da labarin.

KURAKURAI...

Fim din ya tsaru yadda ake so kurakuran dake chiki ba su da yawa ba su wuCe na rashin nuna makomar kananan yaran da aka bari a hannun wannan karamar yarinyar da tace zata kula dasu ba, ya kamata ace a karshen fin din an nuno su

Sannan a karshen fim din lokachin da kungiyar kiristochi suka kawo musu taimako a jirgin ruwa bai kamata yaki binsu ba

Lokachin ake shigar dasu inda Za'a hallaka su acikin matan da suke shafa musu shudiyar kala an nuno wata mata sanye da rigar zamani a a maimakon rigar mutanen daji.

Wannan Kenan Daga abun da na nazarta bayan na kalli fim din.

Shaikh farouq Tukuntawa

Whatsapp me here
08135079888
No comments:
Write Comments