Thursday

Home Rikici : Iran ta tarwatsa Jirgin leƙen Asiri na Amurka.
Da safiyar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2019 Kasar Iran ta baro jirgin leken asirin kasar Amurka yayinda rikici ke cigaba da kunno kai tsakanin manyan kasashen guda biyu.Yayinda jami'an tsaron kasar Iran na ikirarin cewa jirgin Amurkan ta shiga huruminta shi yasa suka barota, amma jami'an Amurka sun ce ba haka bane, jirgi bata shiga hurumin Iran ba a lokacin.
Har yanzu ba'a menene gaskiya lamarin ba.

KU KARANTA: Daga karshe : An Yanke shawarar korar Abdul-aziz Yari daga Jam'iyyar APC. 

Shafin labaran jihar Hormozgan tace:
"Mun baro jirgin leken asirin kasar Amurka. Mun barota ne lokacin da ta shigo hurumin kasar Iran kusa da Koumobarak."

Wannan abu da ya faru shine fito-na-fito na farko tsakanin Iran da Amurka yayinda aka fara cacan baki tsakanin kasashen guda biyu tun hawan mulki shugaba Donald Trump da sanyawa Iran takunkumi.
Amma kasar Amurka ta karyata rahoton Iran cewa an shiga huruminta.


Daya daga cikin abubuwan da sojojin Amurka suka gano a yankin.

Kakakin hukumar sojin Amurka, Bill Urban, yace : "Babu wani jirgin leken asirin da ya shiga hurumin Iran."

Kwamandan hukumar tsaron Iran ya ce wannan abu da kasar tayi sako ne ga kasar Amurka.

Janar Hossein Salami yace Iran ba tasa wani niyyar yaki da wani kasa amma fa shirye take da gwabzawa da kowa.


No comments:
Write Comments