Friday

Home Rikicin jam'iyya: Ana fargabar za a sake dakatar da wani gwamnan APC
Akwai yiwuwar rikicin da ya kunno kai a jam'iyyar APC reshen Jihar Edo sai iya sanadin dakatar da Gwamna Godwin Obaseki

Sai dai magoya bayansa suna ganin gwamnan yana iya samun wata mafita kafin zaben 2020 a jihar

A bangarenta, Jam'iyyar APC ta kasa ta yi tir da irin Obaseki da Bala Mohammed na Bauchi kan ikirarin magudin da aka ce an yi wurin zaben shugabanin majalisar dokokin jihar.

Akwai alamun cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta dakatar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo kamar yadda ta dakatar da Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara.

Wasu hadiman gwamnan biyu sun shaidawa Legit.ng a ranar Juma'a 21 ga watan Yuni cewa suna juyayin abinda zai faru da gwamnan duba da cewa rikicin jam'iyyar APC na jihar yana daukan sabon salo.

A cewarsu, rikicin da ke tsakanin Obaseki da mai gidansa wata shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole zai iya janyo wa jam'iyyar matsala a zaben gwamna mai zuwa.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Ala tilas, Ahmad Lawan ya sallami makiyin Buharin da ya ba mukami. 

"Kamar yadda Cif John Odigie-Oyegun ya fadi a baya-bayan nan, muna fargabar rikicin zai iya janyo wa APC shan kaye a jihar. Sai dai gwamnan ya dauki wannan matakin ne saboda ya gaji da katsalandan da ake masa dama sama," inji daya daga cikin hadiman gwamnan a hirar tarho da akayi dashi.

Da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa gwamnan ya yi zaben 'yan majalisun da ake ganin ya sabawa ka'ida, wani hadimin gwamnan ya ce wannan ba abin damuwa bane saboda Obaseki ya aikata abinda ya ke ganin shine dai-dai duba da yadda wasu ke shirin tayar da tarzoma a jihar.

A bangarenta, Hedkwatan Jam'iyyar APC na kasa ta yi wa Obaseki da Bala Mohammed kaca-kaca kan abinda da ta kira rashin bin ka'ida wurin zaben shugabannin majalisun dokokin jiha a Edo da Bauchi.

Jam'iyyar ta ce zaben shugabannin majalisun da aka yi cikin sirri abin kunya ne ga demokradiyya inji Kakakin jam'iyyar na kasa Mallam Lanre Issa-Oniliu.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments