Saturday

Home Subhanallahi , Yadda wani malami ya rataye kanshi a kano.


Jami'an hukumar 'yan sandan jihar Kano sun bada sanarwar mutuwar wani malamin makaranta, mai suna Femi Oguntumi dake zaune a unguwar Dakata, wanda aka tabbatar da cewa ya kashe kanshi ne.
Har yanzu dai ba a gano dalilin da ya sanya malamin kashe kanshi ba.

Mutumin mai shekaru 40 a duniya, wanda yake ma'aikaci ne a Kwalejin Karish, dake unguwar Kawaji, an iske shi ya rataye kanshi a jikin rufin dakin shi.

KU KARANTA: A Kano: Budurwa ta kashe kanta saboda an saki Mahaifiyarta. 

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, ya ce yanzu haka sun kai gawar marigayin asibitin Murtala domin gabatar da bincike akan shi.

Ya kara da cewa jami'an su sun fara gabatar da bincike akan dalilin da yasa Femi ya rataye kanshi.

Ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari na kisan kai ba, a lokuta da dama akan iske mutum ya sha guba ko ya rataye kanshi, inda wasu suke alakanta hakan da yawan damuwa da kuma bakin talauci da mutane ke fama dashi a wannan lokacin.

No comments:
Write Comments