Saturday

Home Tana ƙasa tana dabo : Ganduje da Sanusi ba su yi sulhu ba tukunna - Hadimin Ganduje
Alhaji Abba Anwar, Sakataren yada labarai na gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Ba ayi sulhu ba tsakanin gwamnan da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II duk da cewa anyi taron a ranar Juma'a a Abuja.

Anwar ya bayyana hakan ne yayin wata sako da ya aike wa Daily Trust.

Ya ce, "Tabbas, Gwamna Fayemi da Alhaji Aliko Dangote sun kira taron sulhu da Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi suka halarta sai dai har yanzu gwamnan bai bayyana matsayar sa kan batun ba.

DUBA WANNAN: An Haramata duk wani gangamin taro a kano : Ƴan Sanda. 

"Abinda zan iya tabbatar muku shine har yanzu ana tattaunawa saboda haka mu jira domin sanin matakin da gwamnan zai dauka."

Ya kara da cewa hakimai da yawa da sauran masu rike da sarautun gargajiya sun hallarci taron.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Ganduje ya sake nada Usman Alhaji a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da kuma Shehu Mu'azu a matsayin babban akawun jihar Kano.

Sanarwan nadin na dauke ne cikin wata jawabi da sakataren yada labarai na gwamna, Abba Anwar ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Kano.

Ganduje ya yabawa ma'aikatan biyu bisa hidimar da su ka yiwa jihar tare da shi a mulkinsa zango na farko da ya kare a ranar Laraba.

Gwamna Ganduje ya bukaci ma'aikatan biyu su aiki babu kama hannun yaro domin tabbatar da cewa wannan mulkin ya fi na baya saboda alkawurran da ya yiwa al'umma.

An rushe dukkan masu rike da mukamman siyasa na jihar amma banda wadanda ke da wa'addin aiki kamar yadda dokokin hukumomi da ma'aikatatunsu suka tanada kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.
No comments:
Write Comments