Thursday

Home Yadda Ake Chatting Da Bluetooth ba tare da Data Connection ba : Android tutorial
Bluetooth chat Android Tutorial.
- Android tricks 2020
- Android tutorial 2020
- Best android appS 2020

BARKAN MU DA WANNAN LOKACI DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA.
-
-
Bluetooth Chat ba sabon application bane. An ɗan jima ana amfani da shi, yanzu haka yana nan a playstore inda mutane sama da dubu ɗari suke amfani da shi, sunan wanda ya assasa wannan application Glodanif.
Bluetooth chat Android tutorial
Bluetooth chat Android tutorial

Wannan Application me suna Bluetooth Chat zai temaka maka wajen aika taƙaitattun saƙonni da hotuna, zaka iya chatting da abokanka ta wannan application matsawar bluetooth naku zayi connect, to zaku iya amfani dashi ba tare da internet connection ba.

Musamman ɗalibai zai matuƙar taimaka muku a yayin da babu Wi-fi a makarantarku, matafiya ma wannan application zai taimaka ƙwarai yayin da suke cikin tafiya yayin da suke cikin tsaunuka, koda babu network a wannan waje zasu iya amafani da wannan application wajen isar da saƙonni zuwa ga juna.

Da akwai abubuwa da yawan gaske wanda wannan application yake taimakawa kawai don isar da saƙonni yayin da babu Network a waje.
Idan abokin ka ko ƙawarki bata da wannan application, kuma babu internet connection da zai bada damar sauke wannan app to abune mai sauki zaku iya sharing na app din ta hanyar bluetooth ba tare da wata wahala ba. ku duba matakan da ake bi a saita wannan app a kowacce irin android.

Yadda Ake Amafini da Bluetooth Chat ba tare da Data connection Ba.⤵⤵

YADDA AKE SAITA BLUETOOTH CHAT APP.

1 - Babu shakka ana buƙatar data don sauke wannan  App zuwa kan waya don yin installing. Girman application ɗin 2.4MB ne kawai , akwaishi a playstore , ko kuna kuyi download kai tsaye ta nan Download Here.

2- Bayan kunyi download sai kuyi install, bayan ya gama installing sai ku buɗe app ɗin, da zarar kun buɗe zakuga wajen saka suna, zaɓar colour, idan kuka cike abin da ake buƙata kawai sai ku danna save.
Yadda Ake Chatting Da Bluetooth ba tare da Data Conection ba  Android tutorial, Bluetooth chat Android tutorial

3 - Ku tabbatar ɗaya wayar da kuke son yin connecting da ita , bluetooth nata a kunne yake. Sai ku danna Scan.

4 - Bayan kun danna Scan sai ku duba ɗaya wayar zakuga pairing request ya bayyana akan screen na wayar, sai ku danna "Pair", da zarar kun danna, duka wayoyin biyu zasuyi connected.

5 - To yanzu komai ya zama ready zaku iya fara aika sakonni da hotuna, kai har ma da emojis.


DUBA WANNAN KUMA.

- Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

- Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min

- Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.


No comments:
Write Comments