Monday

Home Yadda Mohammed Morsi ya yanke jiki ya fadi matacce a kotu
Tsohon shugaban kasar Misra (Egypt), Mohammed Morsi, da sojoji suka yi wa juyin mulki a shekarar 2013, ya mutu a kotu, kamar yadda gidan Talabijin na kasar ya rawaito.

Sashen Turanci na jaridar BBC ya rawaito cewar Morsi ya suma a cikin kotu inda ake tuhumarsa da aikata laifin satar muhimman bayanan sirri (Espionage). Shekarunsa na haihuwa 67.

An hambarar da gwamnatin Morsi bayan shekara daya da hawansa mulki biyo bayan wata zanga-zanga mai zafi.

Tun bayan lokacin yake tsare a kotu.
Morsi ne zababben shugaban kasar Misra na farko, ya hau mulki ne bayan an tursasa tsohon shugaban kasar, Hosni Mobarak, yin murabus.

Bayan an tunkude Morsi daga kan mulki, hukumomin kasar Misra sun shiga farautar magoya bayansa da 'yan kungiyarsa ta 'yan uwa Musulmi (Muslim Brotherhood).
No comments:
Write Comments