Saturday

Home Yadda Wani dalibi ya kashe kansa a dalilin sabani da budurwarsa
rikicn da ya kaure tsakaninsa da budurwarsa.

Dalibin mai shekaru 34 ya kashe kansa ne ta hanyar shan maganin kashe kwari wanda aka fi sani da sniper.

Rundunar yan sandan jihar Legas ta tabbatar mana cewa wani dalibi mai shekaru 34 dake karatu a kwalejin kimiyyar kere-kere ta jihar Legas ya kashe kansa bayan samun sabani da masoyiyarsa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bala Elkana a wani zance da ya fitar a ranar Juma’a ya ce, wannan dalibin dai ya kashe kansa ne ta hanyar shan maganin kwari mai suna ‘sniper’ a gidansa dake shiyyar Eyita a Ikorodu.

KU KARANTA: Yadda Rikici ya barke Tsakanin Matan Kannywood Biyu - Akan Dino Melaye.  

Dalibin mai suna Joseph Mayowa yana karantar Hospitality Management ne a kwalejin. Ya kuma mutu ne a safiyar ranar Juma’a.

A cewar Elkana, ofishin yan sandan dake Shagamu sun samu labarin cewa Mayowa ya kwankwadi sniper bayan rashin jituwa ya shiga tsakaninsa da masoyiyarsa mai suna Bolaji Olokodana.

Olokodana, mai shekaru 24 wacce ta kammala karatunta a kwalejin tana tare da mamacin yayin da abin ya faru, a cewar hukumar yan sanda.

An yi kokarin garzayawa da shi asbiti domin a ceto rayuwarsa bayan ita budurwar ta sa tayi ihun neman agaji daga makwabta amma sai dai hakan bai yi wani tasiri ba.

Budurwar tasa ta shaidawa yan sanda cewa sun kwashi tsawon shekara 9 suna soyayya ita da saurayin nata.

“ Ta ce mamacin na yawan bugunta da zarar wani abu ya hada su. Fada ne ya kaure tsakaninsu sai ita kuma tayi kokarin bar masa dakin da suke ciki zuwa wani dakin domin ta takaita aukuwar rikicin.

“ Dawowarta ke da wuya dakin da ta bar shi saurayin nata sai ganin shi tayi rike da kwalbar sniper ya riga da kurbe abinda ke ciki.” A cewar Elkana.
No comments:
Write Comments