Sunday

Home Yadda 'yan sanda suka yi wa wasu masu garkuwa da mutane dirar mikiya a mafakarsu.
Rundunar 'Yan sandan Jihar Neja ta gano wasu gidaje da masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa suke amfani da su a matsayin mafaka a jihar. The Nation ta tabbatar da cewa an gano uku daga cikin gidajen a unguwar Bosso da ke Minna sakamakon bayyanan sirri da mazauna unguwar suka bawa bawa 'yan sanda. Tuni dai 'yan sandan sun rufe gidajen.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an kama mutane bakwai da wasu bindigu kirar AK 47 yayin da 'yan sandan suka kai sumame a gidajen. A halin yanzu 'yan sandan ba su bayar da cikaken bayani kan abinda ke faruwa ba.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal ; Hotuna   

A yayin da aka tuntube shi, Mai magana da yawun 'Yan sandan jihar, Abubakar Muhammad ya ce baya gari saboda haka ba zai iya bayar da wani bayannai ingantattu kan gidajen da aka gano ba. Ya kuma ce duk wani bayani da aka bayar a yanzu kan gidajen zai iya kawo cikas ga binciken duba da cewa ba a kammala binciken ba.

Kakakin 'yan sandan ya ce zai bawa manema labarai cikaken bayani da zarar an kammala binciken. Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Adamu Usman ya shaidawa wasu manema labarai cewa suna kawo tangarda ga binciken inda ya gargadi su da zuwa kusa da gidajen. Sai dai makwabta gidajen da ke aka rufe sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun kai sumame gidan kuma an kama wani adadin mutane.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments