Monday

Home Yanzu Yanzu: Masu ruwa da tsaki a APC sun mamaye fadar Shugaban kasa. : HOTUNA
Sun yi kira ga shugaba Buhari da ya ja jirgin yan Najeriya sannan ya cika alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya.

 Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin inuwar Concerned APC National Stakeholders (CANS) sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da da Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa. Domin matsin lamba kan bukatarsu, mambobin CANS sun mamaye fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 24 ga watan Yuni.

Musamman suka bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya karbi ragamar gwamnatinsa daga hannun na kewaye dashi yayinda ya fara mulki a zango na biyu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wasu daga ciki allunan da suka dauka na dauke da rubutu daban-daban kamar 'Ya zama dole Abba Kyari ya tafi', 'Ya zama dole PMB ya karbi ragamar mulki', 'Muna son sabbin shawarwari ba na tsoffin da suka shafe sama da shekaru 40 a mulki ba', da kuma 'Ya zama dole a karrama kwazo aiki'da dai sauransu.

Masu ruwa da tsaki a APC sun nemi Buhari ya dakatar da Abba Kyari Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotun zabe ta yi watsi da bukatar Atiku da PDP na duba na'urara zabe na INEC  

Kungiyar tace cewa yan Najeriya sun zabi shugaba Buhari ne ba wai Mamman Daura, Ismail Funtua ko Abba Kyari ba Source: UGC Dr Symeon Chilagorom, jagoran kungiyar yayi korafin cewa yan Najeriya sun zabi shugaba Buhari ne ba wai Mamman Daura, Ismail Funtua ko Abba Kyari ba. Sun bukaci Buhari ya karbi ragamar mulki Source: UGC Ya jadadda cewa yan Najeriya ba za su lamunci abunda ya faru a karo na farko ya sake maimaita kansa ba.

DUBA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Sha biyu 12 - AREWA24  

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments