Tuesday

Home Zaben 2019: Daga karshe Jega yayi magana akan rigimar na’urar INEC
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya musanta gabatar da jawabi akan samuwar na’urar ajiye sakamakon zabe a lokacin da ya shugabanci hukumar.

Farfesa Jega a wani sharhi da aka yada a kafofin watsa labarai, an rahoto inda yake cewa hukumar INEC na da na’urar ajiye sakamakon zabe kuma ‘tana aiki,’ ko a lokacinsa.

A wani sakon wasikar waya ga Premium Times ta hannun wani hadiminsa, Farfesa Jega ya musanta bayar da jawabin, inda yake bayyana hakan a matsayin ‘kalaman ganganci.’

KU DUBA KUMA: Kwana Casa'in - Kashi Na Sha daya 11 - AREWA24

Ya bayyana cewa hukumar a karkashin jagorancinsa bata taba aika sakamakon zabe ta na’ura ba.

Duk da musanta lamarin da Farfesa Jega yayi, rigima akan na’urar INEC na cigaba da kewaye kasar.

Hukumar INEC duk da haka ta dage cewa bata yi amfani da na’ura ba wajen aika sakamakon zaben 2019 ba, inda ta alakanta lamarin da jinkiri da aka samu wajen sakin kasafin kudin hukumar na 2019.

Solomon Soyebi, daya daga cikin kwamishinonin INEC na kasa a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni, yace sabanin cece-kuce da yamadidi da ake yi, hukumar bata aika sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 zuwa na’urarta ba.

Haka zalika, yace hukumar INEC tayi gwajin na’uran wajen aika sakamakon zabe a zabukan Anambra, Sokoto da Osun da aka gudanar kafin zabukan 2019, inda ya karfafa cewa ba ayi amfani da fasahan ba a zaben 2019.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments