Wednesday

Ctrl: da shine ake amfani wajen baiwa computer umarni, Shift: ajikin keybord akwai alamomin da suke kasan madannai misali ajikin lamba 5 akwai alamar % to ina son na dannan alamar % amman idan na danna sai naga lamba biyar ta fito, amfanin shift anan shine zaka danne shi sai kadanna lamba biyar zai baka wannan abin dake kan wannan madannin wanda yaki fitowa, Caps lock: idan ka danna shi kana cewa computer duk abinda ka rubuta to ya fito maka da babban baki sannan idan ka kara danna shi kana nunfin ya fito da karamin baki, Esc: ana danna shine domin fita daga wani guri gaba daya kana ganin computer dinka ta shiga wani gurin da baka gane masa ba cikin hanzari ka danna escape zai fito da kai, Space bar: shine madannin da yafi ko wanne girma a computer ana dana shi ne domin bada space acikin rubutu, ko kuma in kana kallo ko sauraran abu ka dannan domin tsayarwa ko cigaba. Backspace: ana dana shi domin goge rubutu ko komawa baya, Enter: ana danna shi domin shiga waje tamkar “ok” a waya Right click:- domin bada option ko shiga guri Left click:- domin yin selecting highlighting START MENU: Na danyi bayanin a sama da yadda ake shigar sa, shi start menu anan ne zaka ga dukkan program din da kake dasu da mahajojin da kake dasu akan computer ka acikin sa zaka ga All Program shima idan ka shiga zaka gan su, abinda ake cewa manhaja shine software ga masu amfani da wayoyi zasu fi ganewa in ance application to kamar yadda waya take da application to itama computer tana da nata shina ake kira software, Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba
No comments:
Write Comments